Shararren dan wasan Hausa Fim Adam Zango zai koma karatu - Zango yace shi ba dan Luwadi bane Jarumin fina finan Kannywood, Adam Zango yace babban burinsa a rayuwa bata wuce ya kara ilimi wajen magana da harshe Turanci ba, kamar yadda ya shaida ma gidan rediyon BBC Hausa. Shahararren dan wasan, ya bayyana cewar ya kusan dakatar da harkar Fim, inda yake bukatar daga mata kafa domin ya koma makaranta domin karo karatu, musamman yanzu da wasu ke mai kallon jahili.

Img©naij Nayi karatun Boko, sa’annan ina da ilimin addini, kuma a yanzu haka ina son cigaba da karatu na, akalla in samu kwalin Difloma, amma burina shine na iya Turanci sosai da sosai.” Inji A Zango. Dangane da zargin luwadi da ake yi masa kuwa, A Zango ya bayyana ma majiyar NAIJ.com cewa shi ba dan Luwadi bane, kuma bai taba luwadi ba, sa’annan wannan zargi mara tushe na bata masa rai, wanda ya taba janyo hana bashi matar aure.
No comments:
Post a Comment