T Wani mutumi yayi sanadiyar mata sama da 100 sun yi juna-biyu - Wannan abu ya faru ne a can Kasar Nederlands a kasar Turai Wani Bawan Allah ya haifi 'Ya 'ya sama da 100 kamar yadda mu ka samu labari daga wata Jaridar kasar waje. Masu bada ruwan namiji domin a samu juna Labarin wani mutumi ya zo mana game sa wani mutumi da ya samu yara sama da 100 a Duniya. Wannan Bawan Allah ya rika bada kwayan haihuwar sa ne a asibiti ga wadanda su ke bukatar haihuwa ba tare saduwa da namiji ba. Sai dai wannan mutumi ya saba dokar da ke Kasar Netherlands na bada ruwan namiji a asibiti. Wannan mutumi ya bada ruwan na sa a asibitocin kasar har 11 inda yace shi so yake ya ga a sanadiyyar sa an samu yara da dama a Duniya wanda hakan na burge sa. Kwanaki Gidan BBC tayi hira da wani mutumi 'Dan kasar Ghana da ya haifi 'ya 'ya fiye da 100 a Duniya kuma yace har yanzu bai gaji da samun yaran ba.
No comments:
Post a Comment