
HUKUNCIN MATAR DA AKA SAKETA KAFIN SADUWA : TAMBAYA TA 2259 Assalamu alaikum malam da farko dai inamiqa sakon gaisuwa ga malam ina da tabbaya ne MACE CE MIJINTA YA SAKETA SAKI DAYA KUMA BASUFI SATI BIYU DA AURE BA AMMA BA ABIN DA YA SHIGA TSAKANINSU NA DAGA SADUWA TA SUNNAH. SHIN MATAR ZATAYI IDDA NE KO ZATA IYAYIN WANI AURAN KAFIN KWANA ARBA IN KOKUWA ZATA IYA KOMAWA GIDANSHI KODA BAYAN KWANA ARBA'IN DIN? DAGA WATA BAIWAR ALLAH NAGODE BISALAM. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Matar da aka saketa ba tare da an taba saduwa da ita ba, Babu iddah akanta. Saboda fa'din Allah (SWT) : "YA KU WADANDA SUKAYI IMANI, IDAN KUKA AURI MATA MUMINAI SANNAN KUKA SAKESU TUN KAFIN KU SHAFESU (WATO TUN BAKUYI JIMA'I DASU BA) TO BAKU DA WATA IDDAH AKANSU DA ZASUYI.. " (Suratul Ahzab ayah ta 49). Za'a bata rabin sadakinta da akayi alkawari (Idan alkawari ne) idan kuma an riga an bata, to zata dawo da rabi Amma yin afuwa yafi. Kuma zata iya yin aure koda acikin Makon da aka saketa ba sai tayi wasu kwana arba'in ba. Shima Mijin nata wanda ya saketa ya halatta yace ya mayar da ita. WALLAHU A'ALAM. -ZAUREN FIQHU
No comments:
Post a Comment