Thursday, August 24, 2017

Hamshakin Attajirin nan, Aliko Dangote zai gina jami’ar kimiyya da fasaha a Abuja


Hamshakin Attajirin nan, Aliko Dangote zai gina jami’ar kimiyya da fasaha a Abuja Fitaccen attajirin nan Alhaji Aliko Dangote ya kammala shiri tsaf na gina wata katafariyar jami’a a babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito. Tsohon babban sakataren hukumar kula da jami’o’in Najeriya wanda shine shugaban kwamitin samar da jami’ar,Farfesa Julius Okojie ya bayyana cewar manufar kafa jami’ar ta Dangote shine don habbala ilimin kimiyya, bincike da kuma inganta tattalin arziki.

Farfesa Julius ya bayyana haka ne yayin wata ziyara da kwamitin ta kai zuwa ga hukumar kula da jami’o’in Najeriya inda suka gana da babban sakataren hukumar, Farfesa Rasheed Abubakar.

LATEST SPORTS GOSSIP WEDDINGS CELEBS HAUSA NEWS ANNOUNCEMENTS FEEDBACK 367 USD/NGN Kashedi! Yanzu haka Sojin Najeriya na bibiyar abunda kuke yadawa a dandalin sada zumunta Advertise with us Hamshakin Attajirin nan, Aliko Dangote zai gina jami’ar kimiyya da fasaha a Abuja Author: Muhammad Auwal UPDATED: 5 HOURS AGO VIEWS: 2222 Category: News SHARE ON FACEBOOK SEND VIA EMAIL SEND ON WHATSAPP SHARE ON FACEBOOK SEND VIA EMAIL SEND ON WHATSAPP Fitaccen attajirin nan Alhaji Aliko Dangote ya kammala shiri tsaf na gina wata katafariyar jami’a a babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito. Tsohon babban sakataren hukumar kula da jami’o’in Najeriya wanda shine shugaban kwamitin samar da jami’ar,Farfesa Julius Okojie ya bayyana cewar manufar kafa jami’ar ta Dangote shine don habbala ilimin kimiyya, bincike da kuma inganta tattalin arziki. KU KARANTA: Zauna gari banza ýan ƙwace sun shiga hannun jami’an Ýansanda a jihar Legas Farfesa Julius ya bayyana haka ne yayin wata ziyara da kwamitin ta kai zuwa ga hukumar kula da jami’o’in Najeriya inda suka gana da babban sakataren hukumar, Farfesa Rasheed Abubakar. Aliko Dangote A yayin ziyarar, har da shugabar gidauniyar Dangote, Zouera Yousouffou wanda ta bayyan cewa sun ware naira biliyan 200 don gina jami’ar, kuma tace za’a tabbatar da an samar da dukkanin abinda dalibai ke bukata a jami’ar don saukaka musu yanayin karatu. A nasa jawabin, shugaban NUC, Farfesa Rasheed ya yaba da kokarin Dangote, sa’annan yayi alkawarin basu duk gudunmuwar da suke bukata, sai dai ya basu shawarar gara su gina jami’a ta gama gari, amma sai su baiwa bangaren ilimin kimiyya muhimmanci, ba wai jami’iar kimiyya kadai ba. Da take nata jawabin, Zouera Youssouffou tace a shire suke su fara gina wannan jami’a, inda tace sun ware naira biliyan 200, ta kara da cewa tuni har sun sayi filin da za’a gina jami’ar a kai a Abuja.

No comments:

Post a Comment

Pages