Monday, August 28, 2017

Dr. Isah Ali Pantami ya lashe muhimmiyar kyauta a Landan


Dr. Pantami ya lashe muhimmiyar kyauta a Landan Shahararren malamin addinin islama din nan kuma zakakurin mai ilimin sadarwar zamani wanda kuma yanzu haka yake shugabantar hukumar gwamnatin tarayya dake habaka fasahar zamani watau NITD a takaice Dr Isa Ibrahim Ali Pantami ya lashe wata muhimmiyar kyauta a birnin Landan. Shahararren malamin dai wanda dama can tuni daya daga cikin yan kungiyar na ma'abota na'ura mai kwakwalwa a kasar Birtaniyar ya lashe kambun wanda yafi kowa habaka harkar sadarwar zamani a duniya na wannan shekarar.

NAIJ.com ta samu cewa sauran mutanen da suka lashe kyauta a taron dandalin sun hada da Gwamnan jihar Filatoi Plateau da ya lashe kyautar "gwarzon gwamnan shekarar" sai kuma karamin ministan albarkatun man fetur watau Dr. Ibe kachikwu a matsayin "gwarzon ministan shekara". Sauran wadanda suka lashe kyauta a taron sun hada kuma da kamfanin rukunin kamfanonin Dangote a matsayin yan kasuwar shekara sai kuma Sanata Hope Uzodimma wanda ya lashe kyautar dan majalisar shekara.

No comments:

Post a Comment

Pages