Wednesday, August 2, 2017

Batun Rawar Hadiza Gabon Tsirara ›

BATUN RAWAR HADIZA GABON TSIRARA
wani bidiyo ya bayyana da Sunan hadiza gabon ce tayi Rawa tsirara wasu suna ganin itace wasu suna ganin ba ita bace Haka dai wasu suke cewa ya kara tabbatar da
itace.domin an bayyana surarta da. fuskarta
harzuwa tafin kafarta.sannan akwai wani gilas
da take yawan sawa idan zata fita wani wajen
Sannan sukace ita kanta Hadiza har
yanzu bata karyata ba.
Haka ma wani ya shaida mana wannan rawa
tsirara Hadiza gabon ce tayi. Yace Babu wata majiya mai kyau da ta bayyana
Hadiza Gabon ta bayyana ba ita bace. Wanda
sanin kowane duk wanda ake zargi da aikata
masha'a matsawar bai aikata ba, to fitowa fili
yake ya kare kanshi koda baza'a yarda ba. Amma
ita Hadiza shiru ake ji taki kare kanta. Tayaya
baza ace ita bace?
Amma daga bangaren jaruman fina finan Hausa wani jarumin Hausa Fim yace
sabanin fahimta ne akan zargin da akeyiwa Hadiza
Gabon na rawa da tayi tsirara.
Yace wannan karyane akayiwa Hadiza Gabon, kuma hadin kwamfiyutane kawai,
amma ko kama da ita basuyi ba. Domin waccan ba bahausa bace ma, yaci gaba da cewa komai aka kwaso sai anufo 'yan Fim dashi wannan sharrine ai Hadiza ba mahaukaciya bace. Haka dai wasu sukai ta gardama akan bidiyon Sakamakon yada jita jitar da akeyi akeyi da kuma musu akan rawar Hadiza Gabon cikin ikon Allah rumbun kannywood ya samu damar zantawa da Hadiza Gabon ga yadda hirar tasu ta kasance:
Muna ganin wani bidiyo da sunanki Wanda kike rawa a club har kina cire kayan jikinki zamuso muji gaskiyar lamari??
Ai ina tunanin ko ni arniyace bazan iya yin hakanba, komai za'a bani, sannan yaren da akeyi a wurin kamar Spanish Ne ko Mexican, ba yaren najeriya ko Niger, ko Gabon bane, sannan nafi wannan tsinanniyar girman jiki da sauran abubuwa, duk da yake abin mamaki ta kusa yin kama dani a fuska, amma bani bace ba. Bazan taba lalacewa irin haka ba.
Gabon ta ci gaba da cewa:
Nidai nasan bani bace kuma Allah da ya halliceni yafi kowa Sani, saboda haka ina ganin dani dakai duk musulmai ne ya kamata kayarda da abinda Na fadimaka.
Gabon ta yi kira da masu tura Bidiyon da su ji tsoron Allah sannan ta ce
Allah (SWT) a cikin hujurat ayata shidda yana cewa idan munafukai sukazo maku da labari Ku tantanceshi kafin Ku gayawa wasu. Kamar dai yadda ka tuntubeni din nan a matsayinka Na Dan jarida, don haka masu turawa din nan da sunbi wannan ayar sun tantance Labarin da ba suje suna turawaba, sannan mummunan abune yada tsiraci masoyana Su Sani bani bace, makiyana kuma suji Tsoron Allah Su Sani Allah ya tsare mutuncina bazasu iya zubar min dashiba

-Rumbunkannywood

No comments:

Post a Comment

Pages