Duk da haka, a cikin abin da ya bayyana mai karkatarwa,ba barayin da aka sani da sata su ka shiga gidan ba , amma jami'an tsaron da aka sanya su tsare gidan su suka shiga su kayi satan.
A Najeriya 'yan sandan sun kama jami'an tsaron da suka sata abubuwa mai daraja da dama wanda zasu kai miliyoyin naira daga Abuja mazaunin tsohon shugaban kasar. 'Yan sandan sun saci abubuwan ne daga gidan da yake a No. 89, Fourth Avenue a gundumar Gwarimpa da ke garin Abuja.
Sun hada da setin kujeru, tilbijin da dama, firji, su AC da akwatin-lodi na tufafi kamar zanen kara mai dauke da sunan tsohon shugaban kasar,kayan gargajiya na namiji da mace, yadin leshi da huluna.
PREMIUM TIMES na musamman sun tabbatar cewa jami'an 'yan sandan su uku suka gudanar da satar na tsawon watanni uku tun daga kusa Maris 2016, har sai da suka kaucewa kwashe komai da za'a iya fitarwa daga gidan, abin da suka sayar rarrabe zuwa dillalai a Panteka,kasuwar gwanjo, a tashar babbar mota, Gwarimpa. Kakakin Mista Jonathan, Ikechukwu Eze, ya tabbatar da sata ma PREMIUM TIMES. Ya kuma tabbatar da cewa an kama jami'an da abin ya shafa.
Read more: ko kunsan halinda shugaba buhari yake ciki
A cewar wata majiyar tsaro da hannu a gudanar da bincike, a lokacin da 'yan uwa na tsohon shugaban kasar suka ji batun satan a wannan watan, an riga an yaye komai dake a gida. Bincike ya bayyana cewa an gano satar ne a lokacin da wani makwabcin ya lura da"mai tsanani lalacewar da gidan" da kuma kiran wani memba na Mista Jonathan ya tambaya ko gidan na kan gyara ne. Bayan wata tawagar jami'an ta tura zuwa wajen dan tabbatar da laifin, Mr. Idris ya bayar da umurnin da a kama 'yan sandan su uku. "An kama su ne a makonni biyu da suka wuce," dan sandan da yasan tushen binciken ne ya gaya ma jarida a ranar Talata da ta gabata.
SAYAR DA DUKIYOYIN JONATHAN
A Lokacin da PREMIUM TIMES ta samu labaru ta tafi zuwa ga kasuwar tashar baban mota,duka siya da siyarwan ba'ayi shi a boye ba, kamar yadda da yawa daga cikin yan kasuwa suna sane da raban. "A duk lokacin da musamman ko takamaiman abubuwa na sha'awa da aka kawo don sayarwa daga gidan Mista Jonathan, muna saya daga wurin wanda ya sayesu dayawa," wani mai ciniki ce. Bincike ya nuna cewa PREMIUM TIMES tayi bincike akan farashin da suka siyar da wasu kayayyakin.Babban riga da wasu yadudduka sun siyar da su akan farashin naira dubu biyar. Wani dan kasuwanci ya ce ya halarta sayar da daya daga cikin setin kujeru. "Dan sandan ya sayar da daya daga cikin kujerun akan N50, 000,00.Shi kuma mai siyan ya sayar da shi a N180,000.00 shi kuma wannan ya sayar da shi a N390,000.00. "Ni da kaina na sayi Babban riga, da kuma wani kwat da wando mai dauke da sunan Jonathan a kudin N5,000.00 kowane.
" JERIN TUFAFIN DA AKA SACE AKA SAYAR
1. Kayan gargajiya na Neja Delta a cikin ghana must go guda ashirin
2. Suits, kowane daya tare da "Shugaba Jonathan" rubuce a ciki gefen, a cikin ghana must go guda biyar
3. Lasuna,da wasu kayan mata dinkin Neja Delta a cikin babban ghana must go guda goma. 4. Bandul na atamfofi guda goma.
5. Seti goma na Babban riga.
6. Wani babban Ghana must go dake dauke da tufafi da aka rubuta PDP akai.
7. Hulunan Neja Delta guda Ishirin.
KAYAN LANTARKI DA KUMA KUJERU
1. Telebijin 36.
2. Firij 25.
3. Setin kujeru 5.
4. Setin kujeru
2 na falo.
5. A.C kuma da yawa.
-naijhausa
No comments:
Post a Comment