An damfari wani maniyyaci kam kudin sa na guzurin dala
Wani mahajjati dan garin Nasarwa ya bayyana yadda wani ma'aikacin hukumar alhazai ya bashi rabin kudin guzurinsa - Kowane mahajjati ana bashi ambulam dauke da dalar Amurka 'yan dar-dari da sunansa a jiki - Hukumar alhazai zata cikawa Malam Garba kudin guzurinsa Wani mahajjati dan garin nasarawa mai suna Garba Bakono ya bayyana yadda wani ma’aikaci ya bashi rabin kudin guzurinsa maimakon kudinsa duka. Kowane mahajjati ana bashi ambulan dauke da sunan mahajjati da dalar Amurka ‘yan dari-dari guda takwas, saidai ta Malam Garba an musanya mishi babu ma sunansa a jiki bare littafin fasfo. A garin Madina ne Malam Garba ya gana da ‘yan jaridar Premium Times ya fadi yadda wani mai shago yakusa mishi kisan ature da ya je biyan kudin wasu kaya da ya siya. A lokacin ne ya san cewa lallai an danfare shi. Ya fadi sunan wanda ya mishi canjin kudin da suna Hayatu, ma’aikacin Hukumar alhazai ta jihar Nasarawa. Malam Garba yace kwanan su hudu a filin jirgin Abuja kafin su tashi zuwa garin Madina a rananr Lahadi ranar da Malam hayatu mai canjin kudin ya canja musu kudin guzurinsu
Maniyyata 2 na jihar Sokoto sun yi tsintuwar makudan kudi a kasa mai tsarki nan ne ma’aikacin Premium Times ya shaidawa hukumar alhazai masu temako aka tura maganar zua wurin Malam Abubakar Nalaraba dake Makkah. Malam Nalaraba ya kira wani ma’aikacinsu dake madina mai suna Malam Aliyu Aboki wanda ya umarci a cikawa malam Hayatu kudin guzurinsa.
No comments:
Post a Comment