Monday, August 28, 2017

Abin da majalisar dattijai za ta yi game da kalaman kiyayya – Shehu Sani


Abin da majalisar dattijai za ta yi game da kalaman kiyayya – Shehu Sani Sanata Shehu Sani ya bayyana abin da majalisar dattijai za ta yi game da kalaman kiyayya a Najeriya - Sani ya ce majalisar dattijai za ta yi dokoki masu dacewa da za su karfafa ikon hukumomin magance kalaman kiyayya - Sanatan ya ce wajibi ne duk ‘yan Najeriya su yaki kalaman kiyayya a fadin kasar Sanata wanda ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar tarayyar Najeriya, Shehu Sani, ya ce majalisar dattijai za ta yi dokoki masu dacewa da za su karfafa ikon hukumomin wadanda ke da ikon hukunta masu kalaman kiyayya. A cewarsa, zai iya zama haɗari idan aka ba da damar jami'an tsaro su yanke shawara game da abin da ke kunshe da kalaman ƙiyayya ba tare da wani tsari na shari'a ba. Sanatan ya ce: "Majalisar dattijai za ta ba jami'an tsaro samfurin a kan abin da ke kunshe da kalaman ƙiyayya, kuma ba wai kawai 'yan sanda da sojoji suna takura wa masu rubutun ra'ayi a yanar gizon da sauran su”. Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar tarayyar Najeriya, Shehu Sani Ya ce, “Waɗannan daga cikin mu masu gwagwarmaya a lokacin mulkin soja sun san abubuwan da suka faru a wancan lokacin da kuma sakamakon ba da jami'an tsaro izini irin haka”.

"Wajibi ne mu yaki kalaman kiyayya kuma mu kare yancin fadar ra’ayi". NAIJ.com ta ruwaito cewa a kan kafa wani kotun musamman don magance matsalolin kalaman kiyayya, sanatan ya ce: "Kotu na musamman don maganganun ƙiyayya yana da kyau, amma ya kamata ya zama kotu na shari'a ba kotun jeka na fika ba".

-Naij

No comments:

Post a Comment

Pages