Tuesday, August 15, 2017

2019: Ministocin Buhari 7 da za su tsaya takarar Gwamna


Img©Naij

A cikin Ministocin da ka iya fitowa neman Gwamna a zabe mai zuwa na 2019 akwai tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Dr. Kayode Fayemi. Bayan nan kuma akwai wasu. 1.Adebayor Shittu Ministan Sadarwa na kasar ya fada da bakin sa cewa shi zai zama Gwamnan Jihar Oyo mai zuwa. Tun ba yau ba da dama Shitu ya nemi takarar Gwamnan a karkashin Jam'iyyar CPC a baya.

2.Kayode Fayemi Dr. John Fayemi wanda ke Ministan albarku na kasar zai iya kara komawa neman kujerar sa da ya sha kasa a 2014 a shekara mai zuwa da wa'adin Gwamna Ayo Fayose zai kare.

3.Amina Alhassan A zaben da ya gabata Mama Taraba ta kusa kai ga samun kujerar Gwannan Jihar Taraba sai da abin bai yiwu ba. Ba mamaki ta kara jarraba sa'ar ta a shekarar 2019

4.Chris Ngige Da farko ana zaton Tsohon Gwamnan Jihar Anambra Ngige zai nemi takarar Sanatan tsakiya da ya taba wakilta sai kuma bai yi ba. Hakan ya sa ake tunani zai yi takarar Gwamna a zaben bana kuma dai har yanzu da alamu bai da niyya amma ba a ce sam ba.

5.Solomon Dalung Ministan Wasanni Dalung ya taba neman Gwamnan Jihar Filato a karkashin Jam'iyyar adawa ta lokacin. Dalung dan gani-kashe ni na Buhari ne, ko zai kai labari?

6.Dr. Ibe Kachikwu Awai saura irin su Ibe Kachikwu da ake tunani su na da manufar siyasa a Jihar sa ga Delta. Har da wasu manya ‘Yan Siyasa sun faa jan kunnen sa cewa da sauran sa.

7.Hadi Sirika Akwai kishin-kishin din cewa Ministan sufurin jirgin sama na kasar Sanata Hadi Sirika na da niyyar takara Gwamnan Jihar Katsina. Ko ya 2019 za ta kasance?

-Naij

No comments:

Post a Comment

Pages