Satan mutane dai ya zama ruwan dare musamman a hanyar Kaduna zuwa Abuja. Duk da cewa gwamnati ta kara yawan jami’an ‘yan sanda a hanyar abinda kusan kullum sai gaba yake yi ba baya ba.
Yanzu dai ba a hanya kawai ake sace mutane ba har gidajensu ake binsu a sace su. Wasu sukan kubuta da ransu wasu kuma ya kanzo da karewar kwana.
A makon da ya gabata ne wasu matan aure suka kubuta da kyar daga hannu irin wadannan miyagun mutane in da suka zo har gidansu da ke kyauyen sabon Gayan titin Kaduna zuwa Abuja sai dai mijinsu bai tsira da ransa ba domin masu garkuwar sun yi masa ruwan harsashi inda nan take ya sheka lahira.
Su kuma matan sa biyu wanda duk suna shayarwane suka bi barayin cikin kungurmin daji kafin suka bukaci a biya su naira miliya 10 sannan su sake su.
Shi dai garin Sabon Gayan yana kilomita 10 gaba da sansanin horar da masu yi wa kasa bauta NYSC da ke Kaduna. Da PREMIUM TIMES suka zanta da matan bayan an sako su sunce;
“ Kwanakin mu biyar a cikin kungurmin daji tare da wadannan mutane. Duk da sun nemi abasu miliyan 10 ne daga karshe dai bayan munyi ta rokonsu Allah ya dora mu akansu suka yarda a basu naira 100,000.
“ Barayin sun zo gidan mu ne da karfe 12 na dare in da suka yi ta buga kofa, maigidan mu ya ki bude wa. Yayi ta kokari kiran makwabta ta waya da yin ihu amma shiru. Bayan haka dan gaba da mu akwai motar yan sanda amma babu wanda ya kawo mana dauki. Da barayin suka sami nasarar balle kofar sai suka fara yi masa ruwan harsashi inda nan take ya mutu. Suka shiga cikin gidan mu suka kwashe duk abinda ya mallaka sannan suka tafi da mu.”
Matan sun ce barayin sun bar wasu daga cikin ya’yansu biyu a lokacin.
“Shi dai mijinn mu tuka motar itace ya ke yi.”
Bayan haka shima wani manomi mai suna Farouk Mohammed ya gamu da irin wadannan mutane ida har yanzu ya na tsare a hannu masu garkuwar. Sun bukaci a kawo musu naira miliya 1.5.
Yan uwan Farouk sun ce har yanzu suna tattaunawa da masu garkuwar kan a rage musu.
Allah Yakaramana zaman lafiya a kasarmu najeriya
©premiumtimes
No comments:
Post a Comment