A HANYAR KANO ZUWA DAURA AKA BINNE SIHIRIN DA AKAWA Muhammadu Buhari – Aliyu A Jibia
Wani shehin malamin jamia mai suna Aliyu Jibia ya bayana a shafinsa na facebook cewa hakika yana da masaniyar cewa sihiri akawa shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ya kara da cewa a kasar Niger aka yo sihirin kuma aka binneshi a hanyar Kano zuwa Daura.
Malamin ya bayyana hakane a shafinsa inda yace wannan shine amsar da yaba shafin Mikiya.
Ya kara da cewa shine na Farko wajen Sanarda duniya tun a shekarar 2016 amma ba Wanda ya damu da abubuwan da ya tsinkayo.
A cewar Jibia “Ko rubutu na da Na yi Akan Bamagujen Dan Boko ai duk nuni ne Akan Wadanda ke kewaye da Buhari. Kuma sihirin a kasar Niger aka yi shi, amma a hanyar Kano zuwa Daura aka binneshi”.
Ya kara da cewa “Na yi matukar kokari na aikawa Maigirma Shugaban kasa da gudunmawa don warware sihirin ta hanyoyin makusantansa, amma bai je gareshi ba. A karshe, Na gaji, Kuma Na hakura.
Tuesday, July 25, 2017
A HANYAR KANO ZUWA DAURA AKA BINNE SIHIRIN DA AKAWA Muhammadu Buhari – inji Aliyu A Jibia
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment