Sheikh Gumi ya bayyana dalilin da yasa ‘yan Bindiga ba zasu iya aje makamansu ba
Shehin malamin addinin Islama, Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa idan gwamnati bata baiwa ‘yan Bindiga tabbacin tsaron rayuwarsu ba, da wuya su ajiye makamai.
Yace sun shiga daji kuma sun nunawa wadannan Fulani cewa za’a sauraresu, yace kuma Fulanin a shirye suke su ajiye makamansu.
Yace suna da matsaloli irin nasu, baau da ilimi, kuma babu wata kasa da take son zaman lafiya da ci gana da zata bar mutanenta cikin jahilci.
Yace idan dai da gaske gwamnati take ya kamata a yiwa wadannan Fualni Afuwa kamar yanda akawa Tsageran Naija Delta.
No comments:
Post a Comment