Thursday, March 18, 2021

Majalisar Malamai ta kasa ta roki gwamna Gwanduje ya bar Sheikh Abduljabbar Kabara ya ci gaba da wa’azi

 

Majalisar Malamai ta kasa ta roki gwamna Gwanduje ya bar Sheikh Abduljabbar Kabara ya ci gaba da wa’azi 



Majalisar Malamai ta kasa ta roki gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bar Sheikh Abduljabbar Kabara ya ci gaba da wa’azi ta hanyar dage takunkumin da aka saka masa.

 

Sakataren majalisar, Sheikh Dan Azumi Tafawa Balewa ne ya sanar da haka a wata ganawa da yayi da manema labarai a Bauchi. 


Yace kiran ya zama dole lura da cewa Sheikh Kabara na da ‘yancin da kundin tsarin mulki ya bashi yayi Wa’azinsa da kuma walwala. Yace saboda adalci ya kamata a barshi ya ci gaba da wa’azi 


Yace sun ga cewa ya kamata su shiga maganar ne dan kawo maslaha sanna kuma suna girmama banbancin ra’ayi.

No comments:

Post a Comment

Pages