Wednesday, March 3, 2021

Dan adaidaita sahu ya mayar da N2.8m ga fasinja bayan ya tsinci kudin a cikin adaidaitarsa

 Dan adaidaita sahu ya mayar da N2.8m ga fasinja bayan ya tsinci kudin a cikin adaidaitarsa 





- Guled Ibrahim ya fahimci cewa wata mata ta bar makudan kudade a cikin adaidaita sahunsa sannan ya fara neman ta 

- Kuɗin mallakar ɗaya daga cikin fasinjojinsa ne, wata mahaifiya mara lafiya da ya sauke a asibiti tare da ɗanta 


 - Direban adaidaita sahun ya isa asibiti ya tarar tuni ta tafi bayan ta yi kuka game da halin da take ciki An karrama wani matashi saboda gaskiyarsa bayan ya dawo da KSh 815k (N2,827,437.35) ga wata mata mara lafiya wacce ta batar da shi a cikin abar hawarsa.  


A cewar Mustafa Omer, mataimakin shugaban karamar hukuma ta Somaliya a Habasha - wanda ya yada labarin a Facebook, daga baya sai uwar ta fahimci cewa babu jakar da ke dauke da kudin. 


Dan adaidaita sahu ya mayar da N2.8m ga fasinja bayan ya tsinci kudin a cikin adaidaitarsa Hoto: Mustafa Omer/ Deputy chief's office. 


Bayan ta sayar da dabbobinta don tara kudin asibitin dan nata, matar da abin ya rutsa da ita ta kwashe tsawon awanni tana kuka amma daga baya ta bar asibitin.


 Daga baya Guled ya fahimci cewa matar da ya sauke ta manta kudinta a cikin TukTuk sannan ya garzaya asibiti don neman uwar mara lafiyar. Mustafa ya rubuta: "Ba da daɗewa ba aka yi kiran waya aka ga matar; an kawo ta asibiti kuma an mayar mata da kuɗin.


 Ta sake yin kuka: wannan karon cikin farin ciki." Mataimakin shugaban ya ce ya kamata a daukaka irin wannan labarin wanda ke nuna mutuntaka da ladabi tare da karrama shi a tsaka da duk wani mummunan labari. 


A cewar jaridar Ethiopian Today, Mustafa ya gayyaci mutanen biyu zuwa ofishinsa kuma ya godewa Guled da danginsa, sannan ya kara da cewa abubuwan da ya aikata sun nuna kyakkyawan sunan yankin. Matashin direban, wanda rahotanni suka ce ya bar jami’a don tallafa wa danginsa, ya ce abin da ya yi ya samo asali ne daga kyakkyawar tarbiyyar da ya samu. 



No comments:

Post a Comment

Pages