Monday, March 22, 2021

Burutai da sauran hafsoshin tsaro za su bayyana a gaban majalisa kan batun kudin makamai

 Burutai da sauran hafsoshin tsaro za su bayyana a gaban majalisa kan batun kudin makamai 



Majalisar wakilai a Najeriya ta gayyaci hafsoshin tsaron kasa da su bayyana a gaban majalisar 

- Gayyatar ta biyo bayan kamalan mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro a makon jiya 

- Munguno ya bayyana cewa, basu san inda kudin sayen wasu makamai suka shiga ba, wanda ya jawo cece-kuce Kwamitin gaggawa da aka kafa domin binciken kudaden sayen makamai da amfani da su na Majalisar Wakilan Najeriya ya gayyaci hafsoshin tsaro da sauran shugabannin tsaron kasar. 


Shugabannin tsaron za su yi bayani ne game da sayowa da kuma inda aka kwana wajen rabawa da amfani da makaman da aka sayo din a gobe Litinin. 


Jaridar Punch a ranar Asabar ta ruwaito cewa Kwamitin Tsaro na Majalisar ya gana da Ma'aikatar Tsaro kan kudi dala biliyan daya da aka ware don sayen makamai a 2017, wadanda daga cikinsu ne aka biya kudin jiragen Super Tucano guda 12 a Amurka.  


Wannan bincike ya biyo bayan kalaman da mai bai wa Shugaba Buhari shawara kan tsaro Manjo Janar Babagana Monguno ya yi ne a hirarsa da BBC Hausa, inda ya ce ba su san inda kudin makaman suka shiga ba. 


Kalaman nasa sun tayar da muhawara tsakanin 'yan Najeriya, ganin cewa ba wannan ne karon farko da aka zargi shugabannin tsaron da sace biliyoyin kudin makamai ba.


 Shugaban kwamitin, Olaide Akinremi, ya fada wa Punch cewa bayan zamansu na farko sun yanke shawarar binciken kudaden makaman cikin shekara 10 da suka wuce kuma hafsoshin tsaron za su bayyana gaban majalisar a gobe Litinin.  


An bayar da odar makaman ne a karkashin tsoffin hafsoshin tsaro, wadanda Buhari ya sauya a ranar 26 ga watan Janairu kuma ya maye gurbinsu da wasu. Read more: 


Source Legit Hausa

No comments:

Post a Comment

Pages