Tuesday, March 30, 2021

( Bidiyo)Abin da ya sa 'nake koya wa mata kula da al’aurarsu'

( Bidiyo)Abin da ya sa 'nake koya wa mata kula da al’aurarsu' 



Wata likilta ‘yar Najeriya da ke koya wa mata yadda za su kula da al’aurarsu ta bayyana dalilan da suka sanya ta soma wayar da kan matan.

Dr Na’ima Idris Usman, wadda ta kamala karatunta na likita a kasar China a shekarar 2018, ta ce mata da dama suna jefa kansu cikin matsala sakamakon sanya abubuwan da ba su dace ba a cikin al’aurarsu.

Ta bayyana cewa daya daga cikin abubuwan da suka tayar mata da hankali har suka sanya ta soma wayar da kan mata game da kula da al’aurarsu shi ne yadda ake cewa “wai mace za ta iya hada lalle da ruwan kankana ta tura a gabanta”, tana mai cewa hakan ya hana ta barci domin yana da illa sosai ga mace.

Hakan ne ya sa ta ce “ba mamaki yadda mata ke zuwa asibiti ka yi ta ba su magani amma su ci gaba da dawowa asibiti. To, wannan yana cikin matsalolin” da suka haddasa rashin lafiya. 




No comments:

Post a Comment

Pages