Shugaba Buhari ya shaidawa yan bindigan cewa babu wata kungiyar bata gari da ta fi karfin gwamnatinsa
- A cewar shugaban kasar, ba don yan bindigan na iya amfani da yan makarantar a matsayin garkuwa ba da tuni sojoji sun gama da su Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi yan bindiga da ke adabar al'umma a sassan kasar, inda ya ce gwamnatinsa za ta iya yin maganin su.
A cikin sanarwar da ya fitar, mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya ce shugaban kasar ya nuna damuwarsa kan karuwar ayyukan bata gari.
Ya ce idan ba domin ana iya amfani da wadanda aka sace a matsayin garkuwa ba wanda zai haifar da salwatar rayyuka, da tuni jami'an tsaro sun gama da su

No comments:
Post a Comment