Monday, February 15, 2021

Su 7 Sun Yiwa Marainiya Yar Shekara 12 Fyade Sannan Suna Ikirarin Ba Abin Da Za A Musu

 Su 7 Sun Yiwa Marainiya Yar Shekara 12 Fyade Sannan Suna Ikirarin Ba Abin Da Za A Musu 






 Su 7 Sun Yiwa Marainiya Yar Shekara 12  Fyade Sannan Suna Ikirarin Ba Abin Da Za A Musu


Kamar yanda sashen hausa na bbc suka wallafa wasu magidan ta su 7 sun yiwa wata karamar yarinya baiwar Allah mai shekara 12 a duniya Marainiya fyade a jahar Sokoto


 Mahaifiyar tace cikin masu mata fyaɗen akwai wanda ya yi wa ƴarinyar barazanar zai kasheta idan ta sanar a gida.


"Sannan yana mata duka sai kuma ya miƙa ta ga sauran mazan abokan juna, lokacin da aka kama mutum guda a cikinsu da yake duk sun san junansu sai suka rinka tona wa kansu asiri."


Ta ce, "da aka kai su kotu sai aka ce musu ba za a iya yanke hukunci yanzu ba, sai dai a tura su gidan yari zuwa lokacin da za a miƙa shari'ar ta su babban kotu".


"Sai dai kafin a je kotun an sake su daya bayan daya kuma sun ci gaba da yawo a cikin unguwa da tutiyar cewa shari'a ta watse babu batun kotu.


Daya cikinsu akwai wanda yake tsayawa a kofar gidana yana mana dariya ba tare da nuna wani tsoro ba."


Wane hali yarinyar ke ciki?


Marainiyar ƴar shekara 12 a cewar mahaifiyarta tana cikin tsangwama da kyara ganin cewa irin waɗannan mutane sun aikata mugun aiki amma babu matakin da aka ɗauka.


Babu wanda zai iya kare ta yanzu. Ta daina fita makaranta da zuwa ko ina ko leƙa ƙofar gida saboda tsangwama.


Akwai samarin da ke barazanar cewa manya sun aikata laifi babu abin da akai musu don haka hadari ne a gareta, in ji mahaifiyar.


Akwai fargabar da iyayenta ke nuna wa kan abin da zai iya faruwa ko halin da yarinya za ta iya faɗawa a nan gaba.


Me yasa aka saki mutanen?


Barris Mansur Muhammad Aliyu, shi ne lauyan da ke wakiltar mahaifiyar yarinyar da ake zargin an yi wa fyaɗe, ya ce mutum shida cikin bakwai da ake zargi sun amsa wannan laifi.


Lauyan ya ce bayan binciken ƴan sanda an naɗi hoton bidiyo a lokacin da mutanen ke amsa sun aikata wannan fyaɗe.


Yanzu dai abin zuba ido a gani shi ne ko wannan marainiya da ire-irensu da ke koke da irin wannan cin zarafi za a bi kadi a ƙwato musu haƙƙinsu.


Hakika idan babu nan akwai lahira, idan kotu baza ta iya kwatowa wannan yarinya hakkin ta ba Allah ne zai kwato mata shi da kansa.

Ya Allah ka isar ma wannan Marainiya.


Ya Allah jefa rayuwar wadannan mutane a cikin kunci kamar yanda suka jefa rayuwar wannan Marainiya

No comments:

Post a Comment

Pages