Friday, February 26, 2021

Rarara Ya Baiwa Tsofofin Yan Film Dubu 50 Kowannen Su



Fitaccen mawaĆ™in nan na siyasa Dauda Adamu Abdullahi da aka fi sani da rarara ya gwangwaje wasu daga cikin tsofaffin jaruman Kannywood mata damaza da kudi har ₦50,000 ga kowannen su.

Daga bangaren tsoffin jaruman maza da suka samu wannan kyauta akwai; Bashir Na Yaya, Idris Moda, Isa Ja, Sani Garba SK da baba karami. Sannan akwai Shehu Hassan Kano, Usaini Sule Koki, Ashiru Nagoma, Bankaura, Baba Hasin, Kal’uzu Jos da Baba Sogiji.

Bangaren mata kuma sun hada da Hajara Usman, Ladidi Fagge, Hadizan Saima, Ladi tubeless, Saima Muhammad da Asma’u Sani. Sannan akwai Mama Tambaya, Hajiya Sadiya, Baba Duduwa, Fandi Borno, Lubabatu Madaki da Hajiya Binta Ola.

Mazan Zasu karbi gudummawar kudaden nasu ne ta hannu Tijjani Asase a yayinda su kuma matan zasu karbi tasu gudummawar ta hanun furodusa Abubakar Bashir Mai Shadda.


No comments:

Post a Comment

Pages