Wednesday, January 6, 2021

Shugaban kasar 2023: Tsohon gwamna ya bayyana wanda zai gaji Buhari

 



- Tsohon gwamna, Olusegun Osoba, ya bayyana yarjejeniyar da shugabannin APC suka kulla game da wanda zai shugabanci kasar a 2023 - Osoba ya ambaci yankin kasar da ake sanya ran zai samar da dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Tsohon gwamnan jihar Ogun, Cif Olusegun Osoba, ya bayyana cewa akwai yarjejeniyar da aka kulla a lokacin da aka kafa jam’iyyar All Progressives Congress (APC). 


A cewar Osoba, yarjejeniyar shine dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023 zai fito daga yankin kudu. 


Da yake magana a lokacin da ya fito a shirin Arise Television, Osoba, ya ce yarjejeniyar shine cewa arewa za ta samar da Shugaban kasa a 2015, yayinda Shugaban jam’iyyar zai fito daga kudu. 


“A APC mun samu shugaban kasa tsawon shekaru shida da rabi daga arewa. Shugaban kasar zai shafe tsawon shekaru takwas har zuwa 2023. Shugabancin jam’iyyar ya tashi daga Cif Bisi Akande a kudu maso yamma zuwa ga John Oyegun daga Kudu maso Kudu sannan kuma ya koma ga Adams Oshiomhole, shima daga kudu maso kudu. “Tabbas, a karshen wa’adin mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, yarjejeniyar shine cewa Shugaban kasa zai fito daga kudu kuma idan ina maganar kudu, kudu maso kudu, kudu maso gabas da kudu maso yamma na iya samar da shugaban kasa na gaba. 


Don haka, yan kudu maso gabas, kudu maso kudu da kudu maso yamma na iya fito da yan takara don zaben fidda gwanin jam’iyyar kuma duk wanda yayi nasara a zaben fidda gwani na iya zama dan takarar jam’iyyarmu. 

Wannan shine yarjejeniyar da muka kulla a lokacin da muka hade. 

No comments:

Post a Comment

Pages