Tuesday, January 5, 2021

Shekau ya saki faifan bidiyo na farko a cikin 2021, ya gargadi Sheikh Ahmad Gumi

 Shekau ya saki faifan bidiyo na farko a cikin 2021, ya gargadi Sheikh Ahmad Gumi  



Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya saki bidiyonsa na farko a cikin sabuwar shekarar 2021 - A cikin sabon faifan bidiyon, Shekau ya gargadi babban addinin Islama da ke zaune a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi A karo na farko cikin sabuwar shekarar 2021, shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya saki sabon faifan bidiyo tare da yin gargadi na musamman ga babban malamin addinin Islama, Sheikh Dakta Ahmad Gumi.



 Jaridar Daily Nigerian ce ta sanar da hakan a wani takaitaccen sako da ta wallafa a shafinta a dandalin tuwita 



A ranar Lahadi ne Sheikh Gumi, fitaccen malamin addinin Islama, ya ziyarci wasu rugagen Fulani da suka yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja. 


Daily Trust ta rawaito cewa rugagen da Babban Malamin ya ziyarta sun kasance tamkar tarko wurin matafiya a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja. 

Yayin da yake gabatar da jawabi a gaban dumbin al'ummar Fulani a garin Jere, Sheikh Gumi ya bayyana damuwarsa a kan yadda hanyar Kaduna zuwa Abuja ta zama abar tsoro saboda rashin tsaro.  


Sheikh Gumi ya nuna takaicinsa akan yadda duhun jahilci ya lullube kwakwalwar Fulanin da suke garkuwa da mutane domin neman kudin fansa tare da aikata sauran miyagun laifuka. A cewarsa, bawa irin wadannan Fulani ilimin addini ko na zamani shine kadai mafita daga kangin jahilcin da ya jefasu cikin irin mummunar rayuwa. 


A kwanakin baya ne Legit.ng ta rawaito cewa wani mayakin kungiyar Boko Haram da aka kama ya bayyana cewa Shekau ya samu nakasa a kafafunsa, a saboda haka ba ya iya tafiya daidai. 

Matashin mayakin mai suna Mohammed Adam, wanda dakarun rundunar soji suka kama, ya ce Shekau ya samu raunuka a wani luguden wuta da sojoji suka yi a sansanin 'yan Boko Haram. 



A cewarsa, lamarin ya faru ne a yankin Tumbuktu da ke cikin dajin Sambisa, babbar maboyar kungiyar Boko Haram a jihar Borno. 

No comments:

Post a Comment

Pages