Sarkin Zazzau ya yi sabbin nade-nadensa na farko, ya yi sauye-sauye (jerinsu)
Sarkin Zazzau na maye gurbin Iyan Zazzau da ya rasu makon da ya gabata
- Sarkin ya nada kaninsa domin maye kujerar sarautar gidansu da mahaifinsa ya rike
- Wannan ya biyo bayan rasuwar Iyan Zazzau, Bashar Aminu, a jihar Legas Mai martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, ya yi sabbin nade-nadensa na farko kuma ya karawa wasu masu saurauta matsayi a masarautarsa.
An nada Bamalli sarkin Zazzau ranar 7 ga Oktoba, 2020, sakamakon mutuwar Sarki Shehu Idris ranar 20 ga Satumba, 2020.
A jawabin da masarautar ta saki, Sarkin ya maye gurbin marigayi Iyan Zazzau, Aminu Bashar, da dan majalisa mai wakiltan mazabar Zaria, Abbas Tajudden.
Hakazalika, Bammali, ya nada dan'uwasa, Mansur Bamalli, matsayin Magajin Garin Zazzau. Ga jerin sabbin nade-naden:
1. Malam Mansur Nuhu Bamalli - Magajin Garin Zazzau.
2. Abbas Tajjuddeen - Iyan Zazzau.
3. Malam Shehu Tijjani Àliyu Dan Sidi Bamalli - Barde Zazzau.
4. Malam Abdulkarim Bashari Aminu - Talban Zazzau.
5. Malam Buhari Ciroma Aminu - Barde Kerarriyan Zazzau.
6. Alhaji Idris Ibrahim Idris - Sa’in Zazzau.
7. Alhaji Aminu Iya Saidu - Kogunan Zazzau
8. Alhaji Bashir Abubakar - Barden Kudun Zazzau
9. Justice Munnir Ladan - Dan Iyan Zazzau.

No comments:
Post a Comment