Friday, January 8, 2021

Me zai sa ka wallafa hoton matarka a Twitter? An yi cece-kuce kan hotunan auren wasu masoya

 Me zai sa ka wallafa hoton matarka a Twitter? An yi cece-kuce kan hotunan auren wasu masoya 




- Hotunan wasu sabbin ma’aurata ya janyo cece-kuce a shafin Twitter - Yayinda mutane da dama suka yi masu addu’a, wasu sun nuna mamaki kan dalilin da zai sa su neman albarkansu - Miji da matan sun sanya kayayyaki daban daban domin samun hotuna masu ban sha’awa Wasu ma’auratan Najeriya sun je Twitter ta shafin angon domin wallafa kyawawan hotunan bikin aurensu.


 A wani wallafa da yayi a ranar Alhamis, 7 ga watan Janairu, mijin ya je shafinsa na Twitter domin neman albarkar mutane, inda ya bayyana cewa kwanan nan suka raya sunnah. 


A hoton farko, mutumin ya sanya kwat da wando inda ita kuma matar ta sanya doguwar riga ta zamani launin namijin. A sauran hotunan sun yi shiga ta gargajiya ne. 



A daidai lokacin wannan rahoton, hotunan ya samu kimanin mutum 6,000 da suka ziyarce shi tare da sharhi daban-daban daga mutane. Ga wasu daga cikin martanin mutane a kasa: @SquareUmar ya ce: “Ta yaya mutum da ya yarda da Allah zai ci gaba da kasancewa cikin imani alhalin hotunan matarsa na yawo a duniya sannan mutanen kirki da bata gari suna nuna sha’awarsu a kai? Allah ya kare mu.” 


@iam_boas yace: “Allah ya albarkaci auren ya dan uwana.


 Fatan alkhairi.” @KabiruGbadebo ya ce: “Allah ya sanya jin dadi, zaman lafiya, kauna da albarka a wannan gida. Yallabai, miji ka so matarka. Yallabiya, mata ki kaskantar da kanki ga mijinki. 

Wannan shine tsarin a takaice.” @HafizWalii ya ce: “Amarya da ango kun yi kyau, ina addu’an Allah ya albarkacci gidanku da so, zaman lafiya Bijahi Rasululah.” @ba55ey ya ce: “Ina yi maka fatan farin ciki a rayuwar aurenka yallabai!” A wani labari na daban, wani matashi dan Najeriya ya bar jama'a a kafar sada zumuntar zamani cike da mamaki bayan ya bada labarin rabuwarsa da tsohuwar budurwarsa. Ya ce ta bashi na'ura mai kwakwalwa kyauta a ranar zagayowar haihuwarsa domin ya fara damfara a yanar gizo. Kamar yadda ya bayyana a labarin, ta ce bata jin dadin albashinsa domin baya isarsu. Don haka ta bashi kyautar ne don ya shiga gungun wasu masu damfarar yanar gizo. 

No comments:

Post a Comment

Pages