Friday, January 8, 2021

Masha Allah! Bidiyon Rundunar Sojin Saman Najeriya Suna Ragargaza Yan Boko Haram

 Masha Allah! Bidiyon Rundunar Sojin Saman Najeriya Suna Ragargaza Yan Boko Haram 



Rundunar sojin sama ta Operation Lafiya Dole ta yi wa ‘yan ta’addan Boko Haram mummunar barna a dajin Sambisa da ke jihar Borno. 


Ta ragargaza maboyar wasu manyan shugabannin ‘yan ta’addan da ke Alagarno wanda aka gano shugabannin ne kadai ke zama a wurin.

Wurin na boye a kasan bishiyoyi kuma yana da nisan kilomita 2.3 arewa maso gabas daga KAFA, inda ‘yan ta’addan ke amfani da shi wurin shirya makircinsu 


Kamar yadda Manjo Janar John Enenche ya fitar a wata takarda ranar Alhamis, 7 ga watan Janairun 2021, an samu wannan nasarar ne bayan ruwan wutar da aka yi wa yankin. 



No comments:

Post a Comment

Pages