Thursday, January 7, 2021

Martanin Rahama Sadau Da Hadiza Gabon Kan Batun Tafiya Dubai

Martanin Rahama Sadau Da Hadiza Gabon Kan Batun Tafiya Dubai 



A yan kwanakin nan dai ne ake yawan tsinkayar hotunan celebrities da yawa dake nuna su a wajajen shakatawa na gurare daban-daban dake Dubai. Yawancin celebrities din sukan yi amfani da kafar sadarwar nan ta Instagram ne wajen dora hotunan nasu a yayin da suke shakatawarsu a Dubai.

Bangaren jaruman masana’antar Kannywood ma ba’a barsu a baya ba inda da yawa daga cikin jaruman musamman ma matasan matan cikinsu suka shiga cikin ayarin celebrities din da a yanzu haka suke ziyarar shakatawa a Dubai din. 



Daga cikin jaruman na Kannywood da muka samu labarin cewa suna Dubai akwai irin su jaruma Hadiza Gabon, Jaruma Rahama Sadau, Fati Washa, Fareeda Waziri (Laila Labarina), Sadeeya Kabala da sauran su wadanda yanzu haka duk suna can Dubai din kamar yadda suka nuna a shafukan su na sada zumunta.

Ana cikin haka ne dai sai kwatsam muka ci karo da wani Bidiyo inda a cikin bidiyon wata jaruma ta fito tana sukar jaruman da suke ta dora hotunan nasu dake nuna cewa sunje Dubai din. Ta nuna cewa hakan kauyanci ne, a sabili da haka su daina damun mutane da cewa su suna Dubai, Dubai din da a cewar ta da N550k dinka zaka iya zuwa. 


Sai dai maganar tata ta bar baya da kura inda a cikin maganganun nata da alamu ta samu kuskuren zance wanda hakan yasa jama’a suke ta yi mata ba’a da lafazin “on dubai, on dubai”. Wasu kuma sun caccake ta inda suka nuna cewar hassada kawai take yima jaruman.

Jaruma Hadiza Gabon, a cikin wani bidiyo da ta saki na kai tsaye a shafinta na Instagram, ta bayyana cewa ita data ga abun dariya ma ya bata, musamman da aka yi maganar dubu 550 inda tace ko kudin da kashe a Desert Safari ya kusa hakan, sannan daga karshe ta bawa jarumar shawara akan cewa ta dena shiga shirgin yara don kada yara su rainata.

A nata bangaren, jaruma Rahama Sadau itama a cikin bidiyon na kai tsaye da ta gudanar a shafinta na Instagram ta bayyana cewa jaruma on Dubai na daga cikin irin wadanda take ganin girmansu take mutuntasu saboda kasantuwar su manya ne kuma ya kamata a mutunta su, a dalilin haka bai kamata ace tanayin irin wadannan maganganu akansu ba.

Dangane da 550k, “Duk wani wanda yake tafiya ai ba sai an gaya maka yadda tafiya ta dawo ba da harma zaka fara maganar 550k, to koda ma ana tafiya da 550k ne? Ni ban ma taba sani ba sai yau. To ka tafi da 550k ka kwana a ina, a titi? “. Inji Rahama Sadau.

“Kuma Wai da ake ta ihun cewa wai celebrities din Kannywood ne suke ta posting din pictures on Dubai, on Dubai, on Dubai, wanda celebrities din duniya da yawa suna Dubai kuma banga wani aibu ba don kazo kayi dora hotunanka cewa kana Dubai, musamman in akayi la’akari da cewa wannan wani lokaci ne da jama’a suka matsu da su yi tafiya kasantuwar cewa an dade ba’a yi tafiya ba.” Rahama Sadau ta kara bayani.

No comments:

Post a Comment

Pages