Thursday, December 31, 2020

Wata Jarumar Fim Ta Ba Yanmata Shawarar Su Fara Soyayya Da Samari Talakawa A 2021

 



Jarumar fina finan kudu wato Nollywood Didi Ekanem ta janyo wani cecekuce a kafar sada zumanta bayan da ta shawarci yan mata kan hanyoyin da su bi a soyayya cikin shekara mai kamawa ta 2021 da ta rage kwanaki kadan.

Jarumar, a shafinta na kafar sadarwar Instagram ta fara da nuna cewa bai kamata a takurawa mace akan irin namjin da ta zaba a matsayin abokin rayuwa ba.



Ekanem ta buga misali da yadda iyaye a baya suke zabar mazajen aure ba tare da duba nakasun rashin kudi ba.

Ta sake bayyana cewa yan matan da basu yi dacen samun mazan da zasu dinga kashe musu kudade ba, kada su dinga sawa sauran mata suna jin sauran maza haka suke.


Idan da iyayen mu mata basu auri talakawan iyayen mu maza ba, to da yanzu ba a same mu ba. Idan kinyi sa’a kin samu namiji mai kula da ke, to kada ki sanya wasu matan suji su basu da sa’a saboda kaddarar kowa akwai bambanci.”

Jarumar ta ce duk da kudi suna da amfani, bai kamata ya zama kashin bayan alakar arziki ba. Ekanem tayi misali da yadda yan mata suka janyo wasu mazan fadawa laifuka duk da sunan neman kudi.

“Kudi yana da amfani amma bai kamata ya zama kashin bayan kyakkyawar alaka ba. Ku daina kiran maza talakawa. In suka zama yan fashi yanzu, ku za ku yi korafi. Idan suka zama barayi a yanar gizo, za kuyi Allah wadai, bazan iya auren barawo ba, amma kuna kiran su talakawa.”

Madogara: Legit



No comments:

Post a Comment

Pages