Bisa al’adar ƙasar Hausa namiji ne yake ganin mace idan hankalinsa ya kwanta da ita sai ya tura iyaye ko manyansa a nema masa izinin har a kai matakin soma batun aure.
Ko da yake a wasu lokutan akwai auren haɗi da iyaye kan yi wa ƴaƴansu don ƙarfafa zumunci ko abota tsakanin iyalai biyu.
Amma kamar yadda Hausawa ke cewa duniya juyi-juyi, kusan a wannan lokaci zamani ya zo da abubuwa da dama inda a wasu lokuta ma mace ke iya ganin namiji ta furta hankalinta ya natsu da shi ko tana fatan ya aure ta.
Wani abu kuma da ke sake jan hankali a wannan zamani shi ne yadda ake amfani da kafar sada zumunta ko intanet wajen neman miji ko mata.
Baya ga shafukan sada zumunta kamar Facebook da su Twitter da Instagram da wasu kan ce anan suka hadu, ana kuma samun shafukan da su aikinsu shine haɗin-aure da tallata bayanan mutum ga mabukacin ko a samu dacewa.
A kwanakin baya-bayanan a shafuka irinsu Northern Hisbiscus na Instagram kana iya iske bayanan mace da kuma irin namijin da take so, wasu kan ce mai kudi wasu kuma mai rufin asiri, ko wacce dai na bayyana irin abun da take so.
Haka zalika a Twitter akwai wani shafi mai sunan Halal Matchmaking, wanda suma ke wallafa bayanan mace ko namiji da sunan neman dacewa ga mai ra’ayi ko sha’awar aure.
Aisha Falke ita ce mai shafin Northern Hibiscus a Instagram da ke wallafa irin wannan bayanai na neman dacewa, a tattaunawarta da BBC Hausa ta bayyana hujjojin da suka sa mata ke neman miji ta shafukan sada zumunta a wannan zamani.
Ta ce duba da yanayi rayuwa da yadda abubuwa suka sauya gaskiya haduwa har ta kai ga an furta so na wahala.
“Galibi za ki ga mace ba ta wani fita ko zuwa wani wurin da za ta iya haduwa da namiji da zai furta yana sonta, akasari irin wadannan mata watakila daga makaranta sai gida ko wurin aiki, sannan ba wai motar haya ko dai wani yanayi za ta tsinci kanta ba, har ta kai ga an hadu, kuma karshenta ba ta da kawaye ma.”



No comments:
Post a Comment