Yadda wani Matashi yi wa 'Diyata fyade - Abdullahi Abubakar
Abdullahi Abubakar mai shekaru 51 a Duniya ya bada labarin yadda wani Saurayi mai shekara 20 ya kwanta da ‘Diyarsa da karfi da yaji.
Wannan abu ya faru ne lokacin da ta je neman itace. Dattijon ya yi hira da ‘Yan Jarida a cikin karshen mako inda ya bayyana cewa wani Matashin Manomi mai suna Mamman Haruna ya yi lalata da ‘Diyarsa wata rana da tsakiyar yamma a gona.
Malam Abubakar yake cewa Matashin ya zargi ‘Diyarsa da wasu kananan yara 4 da laifin yi masa satar masara a gonarsa, wanda su ka karyata nan-take, inda shi kuma ya fisgo guda daga cikinsu.
Daya daga cikin ‘yanuwan wannan yarinya ya fadawa wannan Bawan Allah cewa wani mutum ya kama yayarsu amma ba su yi masa bayanin duk abin da ya faru ba, har sai daga baya ya gane.
Manomin mai shekara 51 ya ce kashegarin abin ya auku ne ya fahimci cewa salon tafiyar ‘Diyarsa ya canza, daga nan ne ya tasa yarinyar da tambaya har ta fada masa cewa an yi mata fyade.
A cewarsa, lokacin da wannan abu ya auku, ya na wajen aiki domin bai bi yaran zuwa roron itacen ba.
Yarinyar ta tabbatar da cewa Mamman Haruna ya cire mata wando, ya yi lalata da ita. Wannan mummunan abu ya auku ne a dajin Garin Shefu Lafiya inda aka yi maza aka fadawa ‘yan sanda.
Da farko Haruna ya yi kokarin karyata wannan kafin hujjoji su bayyana cewa ya yi laifin. ‘Yan Sanda sun taimaka wajen wannan bincike inda yanzu maganar ta tashi daga hannun DPO zuwa babban ofishin ‘yan sanda da ke Gombe. Yanzu dai yarinyar har ta koma makaranta.
Mahaifin wannan yarinya ya ce an yi gwajin cututtuka irinsu HIV/AIDS watau kanjamau da makamantansu kuma an gano cewa wannan Budurwa ba ta dauke da kowace irin cuta a jikinta.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)

No comments:
Post a Comment