Da duminsa: Ba zamu iya sayar da litan man fetur N121.5 ba - Yan kasuwan mai
Kungiyar yan kasuwar man fetur masu zaman kansu wato IPMAN, ta umurci mambobinta su sayar da litan man fetur a farashin N123.5 sabanin ragin da gwamnatin tarayya tayi na N121.5. IPMAN ta yi tsokacin haka ne kan sanarwan hukumar lura da farashin man fetur PPPRA da ta bada umurnin rage farashin, TheNation ta ruwaito. Kungiyar yan kasuwar mai IPMAN ta ce kawai shawara gwamnati ta basu cewa su rage farashin ko kuma su cigaba da sayarwa a N123.5. Saboda haka, kungiyar ta umurci dukkan masu gidajen mai mambobinta su cigaba da sayar da man su a farashin N123.5 kafin kungiyar Depot su yanke shawara kan sabon farashin da gwamnati tayi umurni.
Hakan na kunshe cikin sanarwan da shugaban kungiyar IPMAN, yankin jihar Kano, Alhaji Bashir Danmallam, ya saki ga manema labarai ranar Talata a Kano. Ya ce dukkan yan kasuwan mai dake karkashinsa su bi shawarar ta hanyar da tabbatar da cewa ba'a sayar da litan mai fiye da N123.50 ba.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)

No comments:
Post a Comment