Yanzu-yanzu: Wani dan uwan Buhari ya sake rasuwa
Allah ya yi wa dan uwan Shugaba Muhammadu Buhari, Ibrahim Dauda rasuwa. Ibrahim Dauda ya rasu ne a Daura, jihar Katsina bayan ya dade yana fama da rashin lafiya.
A sakon taaziyar Shugaba Buhari da mai magana da yawunsa kasa Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar, ya ce rasuwar Dauda babban rashi ne ga mutanen Daura. Shugaban kasar ya ce, "Na yi matukar alhinin rashin wani dan uwa na, mutumin kirki da ya nuna karamci da gaskiya a dukkan harkokinsa."
Ya yi adduar Allah ya jikan marigayin kuma ya saka masa da gidan aljanna. Marigayin ya rasu ya bayar yaya masu yawa cikinsu har da Dauda Ibrahim, babban maaikaci a gidan gwamnati da ke birnin tarayya Abuja.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)

No comments:
Post a Comment