Tambaya
Assalamu alaikum
Malam yau ina cikin damuwa, saboda na kwanta baccin rana,
kawai sai na ji mijina ya danne ni, na yi ta kokarin na kwace
amma sai ya ci karfina ya sadu da ni, alhalin muna azumi,
don Allah malam a taimaka min da mafita, Allah ya sanyawa
zuriyarka albarka
.
Amsa
Wa'alaikumus salam,
To 'yar'uwa mutukar yadda kika siffanta, haka abin ya faru, to
babu kaffara akan ki, saboda takura miki aka yi, kuma ba ki
da laifi a wajan Allah , amma shi kuwa ya sabawa Allah, kuma
ya keta alfarmar Ramadhana, kuma dole ya yi kaffara, ta
hanyar 'yanta kuyanga, in bai samu ba, sai ya yi azumin sittin
a jere, in bai samu dama ba sai ya ciyar da miskinai sittin,
kamar yadda ya zo a hadisin Bukari mai lamba ta : 616.

Allah ka tsare mu da aikata irin wannan
ReplyDeleteTo miskinen guda sittin ne kokuma na kwana sittin
ReplyDelete