Saturday, May 30, 2020

Rago ne a raba auren gaskiya, shekaru biyar muna tare amma ya kasa yi mini ciki – Matar aure ta roki kotu

Rago ne a raba auren gaskiya, shekaru biyar muna tare amma ya kasa yi mini ciki – Matar aure ta roki kotu




Wata kotu dake Iseyin a jihar Oyo, ta raba auren wasu mata da miji masu suna Afeez da Abibat Imran wadanda suka shafe shekaru biyar suna tare, inda matar tayi korafin mijin rago ne.


A rahoton da kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya kawo, Abibat wacce ta tunkari kotu, ta ce tayi hakurin har ta gaji, yanzu tana so a raba auren ne kowa ya huta.

“Shekarar mu biyar muna tare. Da farko yana kokari sosai a gado amma kuma ya kasa yi mini ciki, amma yanzu lamarin ya kara lalacewa inda ta kai ga yanzu baya iya tabuka komai a gadon ma.
“Nayi shiru na gaji gaskiya, lokaci yayi da zan cigaba da rayuwa. Zan samu wani namijin da yake da karfi kuma zai yi mini ciki,” cewar ta.

Abibat ta bayyanawa kotu cewa tuni har ta kwashe kayanta daga gidan mijin nata saboda wannan matsala.

No comments:

Post a Comment

Pages