Friday, September 7, 2018

Wata Kishiyar Uwa Ta Jagoranci Y Wa ‘yar Mijinta Mai Shekaru 9 Fyade



Wata kishiyar uwa mai tsananin kishi ta jagoranci dan cikinta da kuma wasu samari uku wajen aikata fyade da kashe ‘yar mijinta a kan idonta.

Jami’an ‘yan sanda a birnin Kashmir na kasar India sun tabatar da cewa, wannan mata da ba a bayyana sunanta ba ta aikata hakan ne saboda tsananin kishin da ke damunta na cewa mijinta y fi kaunar ‘yar kishiyarta.

Wannan lamari dai ya faru ne a ‘yan makonni da suka shige kuma an samu gawar yarin kimanin kwanaki 10 da suka wuce a ranar Lahadin da ya gabata a kan titin Baramulla da ke a yankin Kashmir, kuma yarinyar da aka aikata fyaden akanta shekarunta 9 kacal da haihuwa.
An samu gawar yarinyar a wani daji, dauke da raunika da a ke zaton ta samu daga ruwa asid (acid) da aka watsa mata da kuma sara da aka y mata da gatari.


Wani jami’in dan sanda mai suna Imtiyaz Hussai ya bayyanawa manema labarai cewa, bayan fyade da aka yi wa yarinyar, an watsawa yarinyar asid, sannan kuma kishiyar uwar tata ta shaketa yayin da danta kuma ya sari yarinyar da gatari.

Zuwa yanzu dai an kama mutane 6 da ke da alaka da fyade da kisan yarinyar.
Wannan kisa dai na zuwa ne watanni kadan bayan da aka tsine gawar wata yarinya ‘yar shekara 8 da aka sace aka yi wa fyade kuma aka kashe a watan Afrilu.


No comments:

Post a Comment

Pages