An nada shi a matayin jakadan kungiyar ta NFVCB
- An bayyana bin doka da manufofin gwamnati a matsayin dalilin nada mai jakadancin kungiyar
Kungiyar tantance fina-finai da bidiyo a kasa (NFVCB) ta na jarumin shirya fina-finan Hausa na Kannywood kuma mawaki, Sani Danja a matsayin jakadanta.
Babban darakta na hukumar NFVCB, Alhaji Adedayo Thomas ne ya bayyana hakan a yau, Jumaá, 31 gwatan Agusta.
"Hukumar ma’aikatar ne suka zabe shi saboda ya nuna cewa yana tare da manufofin gwamnati. Hakan yasa shi kaiwa wannanmatsayin sanna kuma yazamo abun koyi ga sauran mutane,” inji Thomas.
Danja wadda ke shirin fito da sabuwar alban dinsa a kasuwa, yace awai bukatar mawaka su gabatar da ayyukansu ta hukumar tantancen fina-finai. “Ba wai sai an saci fasahar aikinka sannan ne zaka ara neman bin doka ba,”cewar shi.
Sabon alban din mawakin na kunshe ne sakon soyayya da hadin kai da kuma sabon rawa mai taken “siren”.
No comments:
Post a Comment