
A ko da yaushe, garkuwar jikin dan adam a cikin aiki ta ke tukuru a kokarin ta na kashe kwayoyin cututtukan da ke shiga jiki a yau da kullum.
Duk da karfin da wannan garkuwar jiki ke da shi, ta na bukatar taimako ta fannin wasu nau’ikan abinci da za a iya ci.
Su wadannan nau’ikan abinci na taimakawa wajen karfafa garkuwar jikin tare da kashe kwayoyin cututtuka da suka samu shiga ( wato bacteria, germs, viruses da sauransu).
Ga su kamar haka:
1. Zuma
A sha babban cokali daya na zuma da ruwan dumi da sanyin safiya kafin a ci komai. Zuma na kashe kwayoyin cutar bacteria da sauran nau’ika.
2. Tafarnuwa
Duk da cewa tafarnuwa ba ta da farin jini a wajen mutane da dama, ta na daga cikin nau’ikan abinci masu karfin gaske wajen kashe kwayoyin cuta. Ta na dauke da wani sinadari mai suna Alicin da ke fita da zaran an tauna ko an daka ta. Wannan sinadari ya na bada kariya ga jiki.
3. Kurkur
A kan yi amfani da kurkur a gyaran fata da magance ciwuka, to amma ba a nan amfanin shi ya tsaya ba. Kurkur na dauke da sunadaren da ke kashe kwayoyin cutar bacteria a ciki tare da wanke shi tsaf. Ana jika shi da ruwa a sha kowacce rana.
4. Man kwakwa
Ma kwakwa na dauke da sinadaren da ke kashe kwayoyin cuta kala daban daban (Bacteria, virus, fungi, yeast) kamar yadda bincike ya nuna. Wannan ne ya sa ya ke da tasiri wajen magance matsalolin fata iri daban daban.
5. Lemon tsami
Banda sinadarin vitamin C da ke cike a cikin lemon tsami, ya na kuma dauke da sinadaren da ke kashe kwayoyin cuta a jiki. Ana matse lemon tsami guda biyu a cikin ruwa mai tsafta ko shayi mai zafi a sha.
6. Citta
Ita ma ta na dauke da sinadaren da ke kashe kwayoyin cuta musamman wadanda ke haifar da mura, tari da sauran matsalolin makogwaro. A kan tauna ta danya ko kuma a nika a tace ruwan a yi amfani da shi ta hanyoyi daban daban.
7. Abarba
Abarba ma ba a bar ta a baya ba wajen kashe kwayoyin cututtuka musamman wadanda suke kama baki, hanci, da makogwaro.
No comments:
Post a Comment