Saturday, June 16, 2018

Yadda Kwalliya Ya Maida Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Yarinya (Hotuna)





Wata mai sana’ar yi wa mata ado da kwalliya mai suna BukkyGeleMua wacce ke zaune a Birnin London a kasar Birtaniya ta yada hotunan wata tsohuwar tukuf da ta yi wa kwalliya.

Bukky ta ce wannan tsohuwa ta zo wajen ta ne domin ta cancada mata kwalliyar a ranar data cika shekaru 96 a duniya.

Kamar yadda kuka sani, kwalliyar zamani na da karfin sauya fasalin mutum ko yaya ya ke. Ya kan mayarda muni kyawu, ya mayarda baka fara, haka zalika zai iya mayarda tsohuwa yarinya kamar yadda muka gani a fuskar wannan mata.

No comments:

Post a Comment

Pages