![](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEiG2IxrZZENFCJPVP6QgUAKuaK_5qJrW3KTBgEbLgEc7IJ6qQVX223uRMuC4VAhK1xXHvhCTBDssE5rrSWSj27XBLD8FJplG2gh4Z6krJBecp8uGbI24nuz1jpTi9SeowHtmVVzpQvL11EK/s640/8600222.jpg)
- A gwamnatin APC, kowa-noma ake so samari su zama
- YA zuwa yanzu tallafi ya fara isowa talakawan manoma
Ministan noma da ci-gaban karkara, Mista Audu Ogbeh, yace kasar nan ta samar da babban ci-gaba ta fannin noma da kiwo, inda a bana kawai, Najeriya ta samar wa da manoma damar tara kudi da suka ninka na bara sau biyu.
Noman dai yana kawo wa jama'a kudin shiga ne ta hanyar sama musu aikin yi da ma damar fitar da kayan kasashen waje, inda ake taya su sayar wa da dala.
A bayanan Ministan, ya zuwa yanzu, a bara kawai, Naira biliyan biyar manoman suka samu daga albarkatun abin da suka noma.
Wannan na nufin an sami ninki kusan biyu in aka kwatanta da na bara biyu, inji Ministan.
Gwamnatin APC ta sha alwashin farfado da martabar noma a idon jama'a da a baya aka yi watsi dashi aka koma cima zaune.
No comments:
Post a Comment