Sunday, June 17, 2018

Kannywood-Sharhin Fim Din ‘Wata Mafita



Suna: Wata Mafita
Tsara Labari: Ibrahim Birniwa
Kamfani: G. G Production
Shiryawa: Abdul’aziz Dan Small
Bada Umarni: Kamalu Sani
Jarumai: Ali Nuhu, Nuhu Abdullahi, Garzali Miko, Fati Shu’uma, Maryam Yahya, Bilkisu Abdullahi, Hajara Usman, Maryam CTB. Da sauransu
Sharhi: Hamza Gambo Umar
A farkon fim din an nuna Amrah (Fati Shu’uma) tana gayawa kawar ta irin tsananin son da take yiwa saurayin ta Sadik (Nuhu Abdullahi) yayin da kawar take fada mata cewa an kusa bikin sadik yanzu ma yana can wajen dinner. Hakan ne ya tunzura Amrah tabi sahun sadik don ganewa idanun ta komai. Da zuwan ta kuwa sai ta tarar dashi tare da wata budurwa a babban hall. Nan take ta soma zazzaga masa ruwan masifa har ya tanka mata sukayi baram baram. Kwatsam sai Amrah ta farka daga barci sai ta gane cewa ashe mafarki take, nan take ta dauko waya ta kira sadik ta gaya masa komai, amma sai ya kwantar mata da hankali ta hanyar nuna mata cewa sharrin mafarki ne amma shi nata ne har abada. Wata rana Amrah tayiwa iyayen ta sallama ta tafi makaranta, a kokarin fitar ta ne suka ci karo da abokin mahaifin yazo gidan, wato Alhaji Ashiru (Ali Nuhu) bayan sun gaisa ta tafi ne sai Alhaji Ashiru ya shiga gidan har yake sanar da mahaifin ta yaga yana bukatar a bashi auren Amrah, mahaifin Amrah bai yi gardama ba ya amince saboda kyakkyawar alakar dake tsananin sa da Alhaji Ashiru.
A bangare daya kuma bayan hafsa ta tafi makaranta sai ta fara biyawa ta wajen saurayin ta sadik wanda bayan sun gama hira ya sanar da ita cewar ta fada a gida cewa zai turo iyayen sa a nema masa auren ta. Dawowar Amrah gida ne ta sanar da mahaifiyar ta yadda sukayi da sadik, a wannan lokacin ne kuma mahaifin ta ya kira ta ya sanar da ita cewar yayi mata miji. Amrah tayi gardama da zabin mahaifin ta don akwai inda Alhaji Ashiru yazo hira wajen sa ta tashi cikin fushi ta bar shi a wajen. Mahaifiyar Amrah tayi kokarin fahimtar da mahaifin Amrah wanda take so amma sai yaki fahimta kuma yaci alwashin idan Amrah bata auri yaron sa Alhaji Ashiru ba zai tsine mata kuma ya koresu daga gidan sa ita da mahaifiyar ta.
Hakan ya sa Amrah ta amince aka yi auren su da Alhaji Ashiru, amma bayan auren ne sai Alhaji Ashiru ya bukaci Amrah ta fadi abinda zai mata wanda zai sa ta farin ciki. Nan take ta fada masa tana so a kawo mata direba. Tun daga sannan ne sadik ya zama direban da zai dinga kai Amrah makaranta kuma ya dawo gidan da Alhaji Ashiru ya ajiye ta da zama. Hakan sai ya bawa sadik da amrah damar sheke ayar su yadda suke so, sunyi iyakar kokarin su don kawar da zargin mutane a kansu domin ko sadik zai kai Amrah makaranta takan zauna a bayan mota ne har sai sunyi nisa sannan ta dawo gaba kusa dashi, amma duk da haka sai da dan Alhaji Ashiru Abubakar (Garzali Miko)ya taba ganin Amrah zaune a gaban mota tare da Sadik hakan yasa ya sha gaban su da tashi motar ya tsawatar musu.
Amrah da Sadik suka soma rayuwa tamkar ta miji da mata domin Sadik bashi da shamaki da ko ina a cikin gidan Amrah kuma yakan zauna da kowace irin suttura, domin akwai lokacin da yake zaune a falling gidan sanye da gajeran wando da karamar riga suna kallon talabijin shi da Amrah, a sannan ne ‘yar Alhaji Ashiru wato Iklima(Maryam Yahya) ta kawo ziyara gidan har tayi korafin ganin sadik a cikin gidan da wannan suttura, bayan komawar ta gida sai ta sanar da mahaifin ta Alhaji Ashiru abinda ta gani amma sai ya gwasale ta bai goyi da bayan maganar ta ba. Bayan wani lokaci Ikilima tana tsaye a titi tana neman abin hawa sai taga Amrah da Sadik sun wuce ta gaban ta a mota hakan yasa ta fara zargin cewa akwai soyayya a tsakanin su, nan take taje wajen wata kawar ta Rahma (bilkisu abdullahi) ta sanar da ita abinda take zargi sannan Iklima ta roki kawar tata akan tana so suyi soyayyar karya ita da sadik.
Bayan wani lokaci sai Ikilima da Rahma suka kawowa Amrah ziyara kuma sukaga sadik a gidan, take anan rahma ta nuna tana son shi har ma ta bukaci ya kaita unguwa, sai hakan yasa ran Amrah ya baci wanda daga bisani suka soma samun sabani ita da sadik. Rahma ta cigaba da fita yawon shakatawa da sadik wanda har wata rana sukayi hotuna kuma bayan sun kawo wa Amrah ziyara Ikilima ta nuna mata hotunan da rahma sukayi da sadik. Hakan ne ya dagawa Amrah hankali har ta shiga daki tana kuka amma sai Ikilima ta biyo ta gaya mata cewar ta gane soyayya suke yi ita da direban ta sadik. Jin hakan ne yasa Amrah ta fusata suka soma rigima da Ikilima har Alhaji Ashiru ya shigo yaci mutuncin Ikilima.
Hakan babu jimawa sai Amrah ta soma rashin lafiya bayan zuwan su asibiti ne aka sanar mata da cewar tana da ciki, a hanyar dawowar ta daga asibiti ne aka kira wayar ta aka fada mata maganar mutuwar mijinta Alhaji Ashiru wanda yayi hatsari ya rasu. Jin hakan ne yasa sadik ya soma murna akan dan su dake cikin Amrah zai samu dukiya amma sai Amrah ta nuna masa cewar bazata ha’inci Alhaji Ashiru ba domin akwai mutimin da yasan cewa juna biyun jikin ta na sadik ne. Jin hakan ne yasa sadik yaje ya kashe mutimin. Amrah tana zaune a wajen zaman makoki sai ta samu labarin mutuwar Alhaji Bala wanda yasan tana da juna biyu. Bayan ta gane cewar sadik ne ya kashe shi sai ta sanar da iyayen ta duk gaskiyar lamari kuma ta fada musu gaskiyar cewa Alhaji Ashiru ya sake ta tun a daren auren su dashi kuma ya shige gaba ya aura mata sadik kuma babu wanda yasan haka sai Alhaji Bala wanda sadik ya kashe. Jin hakan ne yasa iyayen Amrah suka nuna mata ingancin auren ta da Alhaji Ashiru sannan kuma itama Amrah tayi nadamar tarayyar ta da sadik.
Abubuwan Birgewa:
1- Labarin ya tafi kai tsaye ba tare da ya karye ba har ya dire.
2-An samar da gidaje wadanda suka dace da labarin.
3- Labarin ya nuna muhimmanci a kan zabi nagari da iyaye su ke yiwa ‘ya’yansu.
Kurakurai:
1- Amrah ta yiwa iyayen ta sallama akan zata tafi makaranta inda har mahaifiyar ta ta bata sako ta kaiwa kawar ta, amma mai kallo bai ga Amrah ta dauki kayan karatu ba kamar su hand-out ko kuma laptop. Ya dace a nuna dalilin tafiyar ta makaranta babu jaka ko kayan karatu, koda ta hanyar fada da baki ne ace ta manto su a hannun wata kawarta ‘yar ajin su.
2- Amrah ta fita zance wajen manemin auren ta Alhaji Ashiru amma babu hijabi ko mayafi a jikanta, matsayin Amrah na musulma kuma bahaushiya, fitowar ta zaman hira a waje babu mayafi ya saba wa tarbiyya gami da al’ada ta malam bahaushe.
3- Amrah ta fita daga gidan iyayen ta don zuwa makaranta kuma babu jaka a hannun ta, amma sai mai kallo ya ganta rataye da jaka a lokacin da taje wajen da sadik yake aikin wankin mota, shin a hanya Amrah ta hadu da jakar har ta rataya ko kuma kasuwa ta biya ta siya?
4- Bayan auren Amrah da Alhaji Ashiru mai kallo yaga Amrah a cikin dakin ta tayi shirin zuwa makaranta har ta yafa mayafi kalar ruwan hoda ta fita, amma bayan ta fito falo don yiwa mijinta sallama sai aka ganta sanye da koren mayafi, shin mayafin rikida yayi daga kalar ruwan hoda zuwa kore? Bayan kuma ta fito haraba zuwa wajen direbanta sai aka sake ganin ta da mayafin farko kalar ruwan hoda, shin me yake sauya kalar mayafin Amrah?
5- Lokacin da sadik ya dauki Amrah don kaita makaranta inda yake tambayar ta shin yau alhaji a gidan yake? Domin shi ya matsu dare yayi. Motar da aka gansu a ciki kalar ruwan toka ce me duhu, amma bayan ya sauke ta a makaranta sai aka gansu a cikin farar mota. Shin me ya sauya kalar motar daga ruwan toka zuwa fara?
6- An nuna Amrah da sadik a cikin falo inda yake tambayar ta abinda ta girka musu, bayan sun juya sun nufi wajen cin abinci sai kuma me kallo ya gansu a cikin daki a kwance suna hira. Ya dace a samar da dalilin da ya sauya musu ra’ayin cin abinci ya mayar dasu zuwa cikin daki don yin hira.
7- Bayan auren Alhaji Ashiru da Amrah kalaman da Amrah suke yi ita da Sadik sun girmama kuma batsa tayi yawa a wasu daga cikin maganganun nasu. Ya dace su yi maganar cikin azanci ta yadda yara ba zasu gane nufin su ba, domin cikakken magidanci zai ji kunyar kallon fim din tare da ‘ya’yan sa. Idan kuma har ya zama dole batsa ta shigo cikin kalaman su, to ya dace a rubuta doka a fim din ta cewar kada yaro dan kasa da shekaru goma sha takwas ya kalla.
8- Bayan iyayen Amrah tare da iyalan Alhaji Ashiru sun gano cewa Sadik ne ya kashe Alhaji Bala, ya dace aga sun dau mataki akan Sadik koda ta hanyar furtawa da baki ne cewa zasu mika shi ga hukuma, domin kisan rai ba karamun abu bane da al’umma zasu gani basu dau matakin komai ba.
Karkarewa:
Marubucin ya yi kokari wajen gina labarin, amma ya dace a ce ma’anar fim din tafi haka gamsarwa.

No comments:

Post a Comment

Pages