.
Hamshakin attajirin nan Aliko Dangote ya mika wa ‘yan gudun hijira rukunin gidaje 200 da gidauniyar sa ta gina wa ‘yan gudun hijira a Maiduguri.
Cikin wannan rukunin gidaje an gina makarantu, asibitoci, Masallatai da filayen noma da sauransu.
Wadanda suka more wannan abin alheri daga Dangote basu shiga gidajen su haka kawai ba domin har da gudunmuwar naira N100,000 ya mika wa kowa a filin bukin mika musu mukullan gidajen.
” Mu fa bamu da ta cewa, domin Aliko Dangote yayi mana komai a jihar nan. A garemu bayan fannin Shariya, Zartaswa da majalisa wato dokoki toh sai Aliko Dangote.
” Da ya ziyarci wannan jiha a 2016 ya ce zai bamu kudi naira biliyan biyu, sai muka ce ya raba ya kawo mana kayan gini tun awancan lokaci, toh ingaya muku cikin sati biyu an kawo mana wadannan kayan gini.”
” Mun saka wa wannan rukunin gidaje rukunin gidajen Dangote domin kuwa akwai Masallaci, Asibitoci, Makarantu da duk abin da kake bukata domin jin dadin rayuwa.” Inji Gwamnan jihar Barno, Kashim Shettima.
No comments:
Post a Comment