
Jamila Nagudu tayi ikirarin cewa babu sa’arta a yan matan Kannywood
- Ta bayyana hakan ne a wani hira da tayi da sashin BBC Hausa
- Jamila ta kasance gwana a duk matsayar da aka daura ta a kai
Shahararriyar jarumar nan ta Fina-finan Hausa, Jamila Nagudu, ta bayyana cewa babu sa'arta a duk matan da ke harkar fim a yanzu
Saboda haka ita uwa ce a cikin masu harkar shirya fina-finan.
A hirarta da shashin BBC Hausa ta ce kwarewa ce ta sa ta ke iya taka kowacce rawa da aka nemi ta yi a fim.
Kamar yadda kuka sani Jamila ta kasance tauraruwar da aka dama da ita kuma ake kan damawa da ita a masana’antar ta shirya fina-finai.
Hakan ya samo asali ne ga yadda jarumar kan taka rawar gani a duk bagiren da aka daurata yayin shirya wasa.
No comments:
Post a Comment