2019 : Dan Kwallon Najeriya NWANKWO KANU zai Tsaya Takarar Shugabancin Kasa A 2019.
Duba da nasarar da tauraron dan wasan nan na kasar Liberia ya samu na zama zababben shugaban kasar Liberia
Mun samu bayanai dake nuni da cewar shima takwaransa daga nan Najeriya wato tauraron kwallon kafa Nwanko KANU zai shiga sahun zawarawan da zasu fafata a takarar neman kujerar shugaban kasar Najeriya a 2019
KANU Wanda ya sha taimakawa Najeriya kaiwa ga nasarori da dama a wasanni da dama yasha alwashin dora Najeriya akan saiti ta hanyar farfado da tattalin arzikinta ,korar fatara da yunwa,Samar da tsaro,samawa ‘yan aikin yi ,inganta lafiya da ilmi da kuma tafiya kafada da kafada da matasa da sauransu
Koda yake kanu bai bayyana jamiyyar da zai tsaya takara ba
Amma masu nazartar siyasar Najeriya na ganin cewar akwai yiwuwar ya tsaya wannan takara ne a jam’iyyar PDP duba da kyakkyawar alakarsa da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan da kuma rawar da KANU din ya taka a yakin neman zaben na Jonathan a 2015.
Hausawa dai na cewa ba’a San maci tuwo ba sai miya ta kare.
#Arewablog
No comments:
Post a Comment