Sunday, April 8, 2018

A duk lokacin da na dawo gida sai mahaifiyata ta duba budurcina - fitacciyar mawakiya






Shahararriyar mawakiya Tope Alabi, ta bayyana irin matukar sanya ido da haifiyarta ta yi mata, musamman lokacin da ta fara zuwa masana'antar shirya fina-finai.

A wata hira da tayi da gidan jaridar PUNCH NG, mawakiyar ta jinjinawa mahaifiyarta bisa goyon bayan ta kan sana'arta ta kade-kade. Ta ce, da yawa daga cikin y'an uwanta ba sa son sana'ar da take yi, in banda mahaifiyarta.

A irin tarbiyyar da ta samu gurin mahaifiyarta, Alabi ta ce, bai kamata mace ta rinka cakuduwa da maza ba, wanda hakan zai iya haifar da lalacewar tarbiyar mace.


Alabi ta nuna damuwa da irin kallon da jama'a ke musu na marasa tarbiyya tare da yi musu kudin goro. Ba kowa ne lalatacce ba.


A duk lokacin da na dawo gida sai mahaifiyata ta duba budurcina. " Don ta tabbatar da ba ta yi lalata gun koyon kade-kade ba.

No comments:

Post a Comment

Pages