Wednesday, February 14, 2018

NNPC Za Ta Soma Hako Danyen Man Fetur A Jihar Bauchi



Za'a fara tono mai a wuraren da ake kyautata zaton samu a jihar Bauchi. Shugaban kamfanin NNPC na kasa Maikanti Baru ne ya shaida haka yayin da ya karbi tawagar gwamnan jihar Bauchi Barrister Mohammed A. Abubakar lokacin da ya kawo ma sa ziyara.

Shamsuddeen Lukman Abubakar, mai taimakawa gwamnan a harkar sadarwa yace gwamnan ya ziyarci cibiyar NNPC ne don jinjina wa shugaban kamfanin bisa binciken mai da ake yi a wasu yankunan jihar Bauchi.

A yayin da yake jawabi, babban daraktan kamfanin yace an kusa kammala shirye shirye, don fara tono rijiyoyin mai guda biyar a yankunan Alkaleri da ke jihar Bauchi.
Yace hukumar na amfani da fasahar zamani don hako mai a wuraren bisa umurnin fadar shugaban kasa.

Gwamna M.A Abubakar yace a shirye yake ya bada hadin kai don ganin an samu nasara a yunkurin hako man. Wanda idan aka samu nasara, jihar Bauchi za ta kasance cikin jihohi da ake tono mai a Nijeriya.

No comments:

Post a Comment

Pages