Monday, February 12, 2018

Kannywood: Muna shan wahala matuka wajen samun mazajen aure – Rashida Abdullahi



Fitacciyar tsohuwar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood kuma 'yar siyasa mai suna Rashida Abdullahi ta jadadda cewa suna fuskantar kalubale wajen samun mazajen aure.

Majiyarmu ta kawo inda Jarumar ta kara da cewa: “Samun Mazan Ne Da Wahala, Amma Ko Yanzu Na Samu Miji Da Gudu Za Tayi Aure”.

Idan zaku tuna NAIJ.com ta kawo a baya cewa jarumar dai ta janye kafar ta daga fitowa a matsayin jaruma a cikin fina-finan Hausa na Kannywood sannan kuma ta tsunduma cikin harkokin siyasa.

No comments:

Post a Comment

Pages