Monday, January 15, 2018

Wata sabuwa: Kungiyar MOPPAB tace ba ta yafewa Rahma Sadau ba



- Kabiru Maikaba yace ba Afakallahu bane zai yi wa ‘Yar afuwa ba
- Kwanan nan za a zauna da babbar ‘Yar wasan kwaikwayon a Kano
Mun samu labari a makon nan cewa Kungiyar MOPPAB ya ‘Yan wasan Najeriya tace har yanzu fa ba ta yafewa ‘Yar wasan nan ta Hausa da ta dakatar a da can ba watau Rahma Sadau ba.
Kai ya rabu game da yafewa Rahma Sadau Kungiyar MOPPAN ta Jihar Kano ta musanya cewa ta gafarta Rahma Sadau laifin ta kuma an yafe mata ta rika fitowa a fina-finan Kannywood. Shugaban MOPPAN na Jihar Alhaji Kabiru Maikaba yace ba a yafewa ‘Yar wasar ba tukun.
A baya dai Shugaban Kungiyar tantance fina-finan Hausa Isma’ila Na’abba Afakalla yace Kungiyar su ta shirya tantance fina-finan ‘Yar wasar da aka dakatar kwanaki wanda hakan ya sa aka dauka an yi wa Sadau din afuwa ne.
Maikaba ya bayyana sashen Hausa na BBC a yau dinnan cewa kwanan nan za su zauna da ‘Yar wasan bayan ta dawo kasar wajen da ta tafi.
Bayan zaman ne za a san matakin da za a dauka game da Tauraruwar ‘Yar wasar Hausan.

No comments:

Post a Comment

Pages