Ugochukwu Okeke da aka fi sani da Alino ya rasa ransa a hannun matarsa, Chinenye Adaeze Okeke da kuma wani yaronsa bayan ya kamasu suna cin amanarsa ta hanyar lalata Marigayi Okeke dan kabilar Igbo ne daga garin Ndimgbu ta jihar Anambra, kuma rahotannin sun nuna cewa mai dakinsa, Adaeze da taimakon farkanta, wanda yaro a wajen Marigayi Okeke sun lakada masa dukan kawo wuka har sai da ya ce ga garinku nan
Marigayi Okeke dai shi kadai ne a wajen mahaifiyarsa da aka fi sani da Madam Holy-holy kuma yana da ‘ya’ya biyar da mai dakinsa da ake zargin ita ta kashe shi
Adaeze da abokin lalatarta sun nade gawan Marigayi a cikin kyalle, inda suka saka shi a bayan mota da nufin su je su jefar da shi a wani wajen, sai dai suna cikin tafiya a mota don zuwa su yasar da gawar sai ‘yan sanda suka kama su inda a halin yanzu suke hannun ‘yan sandan birnin Yawunde na kasar Kamaru, inda lamarin ya faru
A wani yanayi na ramuwar gayya, dangin Marigayi sun kai hari gidansu Adaeze da ke Mbanagu a ranar Asabar din da ta gabata, inda suka caje gidan tsaf suka kwashe hutunan Adaeze kafin daga baya su cinnawa gidan wuta
No comments:
Post a Comment