Bayan gaisuwa tare da addu'ar Allah ya sa a kammala hutun karshen mako lafiya, ina fatan Allah ya sa haka. Amin.
Na rubuta maka wannan wasika ne domin ankarar da ofishin ka, kan yadda kalaman wani kwamishina mai ci a Kano suka fara haifar da Da marar idanu kuma na ji shiru tun lokacin da wancan kwamishina ya yi wadannan kalamai na tunziri ban ji ofishin ka ya dauki wani mataki na zahiri ba domin yi wa tufkar hanci.
Ina nufin dai irin matakan da kuke dauka akan sauran al'umma musamman barayin akuya ko masu satar biredi idan yunwa ta kawo musu hari.
Ya mai girma kwamishina, adalci ga kowa shine kashin bayan zaman lafiya, rashin sa kuma shine ke haddasa rudani da tashin hankali tsakanin al'umma.
Yau Lahadi fa kalaman da wancan kwamishina da har yanzu ba mu ga kun kira da jin ba'asin kalaman nasa ba sun fara yin tasiri, domin kuwa wasu 'yan sara suka sun afkawa wasu mabiya darikar Kwankwasiya har ma an raunata wasu da dama ga hotan misalansu nan ma na dauko lokacin da na ziyarce su a sashin agajin gaggawa na asibitin Murtala dake nan Kano.
Ba zan tsawaita zance ba tun da na san ka san kalaman da shi wancan kwamishina ya yi tun da an yada su mutane da yawa sun ji sun gani. A zantawar mu da wadannan mutane da aka afkawa sun zayyana min abin da ya faru har sun ambaci sunayen wasu mutane ciki har da masu alaka da shi wancan kwamishina mai kalaman tunziri, amma ba zan ambaci sunayen ba sai nan gaba idan na ji daga bakin su wadanda aka zarga, domin ni ma na kamanta adalci, koda yake na sami bidiyon yadda wannan farmaki ya faru.
Ya mai girma kwamishinan 'yan sanda a lokacin da nake zantawar da wadannan mutane na jiyo wasu daga ciki suna kalaman cewar matukar ba a dauki mataki ba to su ma za su dauki fansa, kuma fa irin wannan ne ba a so.
Ina rokon kwamishina ya yi wani yunkuri domin tabbatar da cikakken bincike domin yi wa tufkar hanci, shi kuma kwamishinan da ya yi wadancan Kalamai lallai a yi masa abin da ake wa duk wanda ya yi katobara irin wannan, wanda yin haka zai sa kowa ya shiga taitayinsa ya ringa yi wa bakin sa linzami koma takunkumi.
Batun wadanda aka sassara a yau kuma, gaskiya abin akwai takaici a ce har yanzu a Kano ba a daina sara suka ba, watakila rashin kama masu daukar nauyin su ne, wannan ma ina so kwamishinan 'yan sanda ya bincika tare da nuna halin ba sani ba sabo.
Allah ya ganar da mu gaskiya ya ba mu ikon bijirewa duk wani dan siyasa da zai tunzira mu mu dauki makamai mu afkawa 'yan uwan mu. Wassalam ka huta lafiya, sai ka ji ni cikin wasika ta ta gaba.
Nine naka Nasir Zango.
No comments:
Post a Comment