Sunday, January 21, 2018

Tsohuwa Yar Shekaru 99 Ta Tsaya Takarar ‘Yar Majalisar A Kasar Malaysia



Wata tsohuwa ‘yar shekaru 92, sannan kuma tsohuwar firaministan kasar Malaysia, Tun Mahathir Mohamad, za ta kasance babu wani dan majalisa dattijai da ya kai ta tsufa idan har ta lashe zaben zama ‘yar majalisar kasar Malaysia a zaben kasar.
Amma yana iya kasancewa akwai wasu tsoffin da suka fi ta tsufa wadanda su ma za su tsaya takara a zaben kasar Malaysia.
Wata tsohuwa, Madam Maimun Yusof, ‘yar shekaru 99, ta tsaya takarar ‘yar majalisar kasar na Majalisar Kuala Terengganu a zaben 2008 da 2013 amma duk an kada ta.
Ta tsaya takarar a matsayin ta na ‘yar kasar ba tare da neman goyon bayan jiga-jigan ‘yan siyasa ba, inda ta yi amfani da symbol 3 a shekarar 2013, wanda ya kunshe manya-manyan kabilu 3 da ke Malaysia wato Peninsular Malaysia’s.
Ta ce za ta sake tsayawa takara idan ta samu kudin malaysia RM10,000 (wanda hakan yayi daidai da kudin Amirka dala $3,350) wanda hukumar zaben kasar Malaysia ke bukatar kowane dan takara ya biya.
“Idan ina da kudi, zan sake fitowa takara,” ta bayyanawa kafafen yada labarai na Malay-language tabloid Harian Metro. “Amma ta yaya? a yanzu haka, Tok Maimun, ba ta da kudi. Za a gudunar da zabe kasar Malaysia a tsakiyar wannan shekarar.
An yi ma ta wata tambaya a 2013 a shafin yada labarai na yanar gizo mai suna Malaysiakini News, a kan dalilin da ya sa ta tsaya takara, kakan ta ce: “Ba abu mai kyau ba ne mutum yayi shiru idan har ya ga yadda ake aiwatar da abubuwa ba daidai ba. Ba za a samu canji ba idan har mutum ya kama bakinsa yayi shiru “Suna so su siyarwa baki da kasan nan amma kuma Tok ba sa so a siyar,” ta ce.
Madam Maimun ta yi da’awar cewa kungiyar musulmai wanda ake kira Parti Islam SeMalaysia, wadanda su ka rike shugabanci yankin Terengganu a kasar na tsawon shekaru 5 bayan zaben 1999, sun so su “siyarwa ‘yan Japan da Terengganu” saboda tambarin farin watan wata da kuma zanen jan zagaye da ke kan tutar ‘yan kasar Japan.
An kada ita a zaben 2008 da 2013, inda ta samu kuri’a 685 a shekarar 2008 da kuma 182 a shekarar 2013, daga cikin kuri’a 60,000. Amma ta samu karbuwa a hannun ‘yan jarida a duk zaben da aka gudunar, tare da postan neman zaben ta a manne a keken hawan ta a jaridu da dama.
Dr. Mahathir, wanda shine abokin takaran ta, ya ce wata kila zai sake tsayawa takarar dan majalisar mai wakiltar gundumar Langkawi ko Kubang Pasu, wadanda suka kasance duk a jihar Kebah.

No comments:

Post a Comment

Pages