Saturday, January 20, 2018

“Mazakunta Na Ya Sa Mata Suka Guje Ni” – Dan Wasan Kwaikwayo, Don Little



Fitaccen jarumin fina-finan Ghana, Don Little, wanda aka fi sani da suna ‘Ghanian Aki’, ya ce rashin girman mazakuntarsa ya sa mata ke rabuwa da shi.
Dan wasan ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke amsa wata tambaya da aka masa a wani shirin gidan talabijin na Adom Tv wanda ke Ghana.
A cewar sa, ba ya iya gamsar da mata wajen biya masu bukatar a yayin jima’i saboda rashi girman mazakuntar sa.
Ya ce, “Mata su kan rabu da ni saboda girman mazakunta na. Su na masu da’awar cewa mazakunta na ba shi da girman da zai biya masu bukata
Jarumin, duk da haka, ya ce ya kwana da mata kusan 5 wadanda suka fi shi tsawo amma duk daga baya sun kasance suna gunguni a kan wannan matsalar na shi.
Don Little ya ce bai cire rai a kan samun irin matan da ya ke so ba, wacce za ta so shi tsakani da Allah a tare da nuna wani bambanci ba.

No comments:

Post a Comment

Pages